24 Faburairu 2015 - 04:34

Jami’in yada labarai na rundunar sayyidu shuhada Iraki yace; wasu sojojin sa kai na kasar sun hari wani jirgin mai saukar angulu mallakar Amurka inda suka tilasta masa sauka.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti{A.S}-abna-Hassan khakani jami’in yada labarai na rundunar sayyidu shuhada yace; sojojin sa kai sun hari jiragen mallakar Amurka yayin da yake kokarin kai ma yan ta’addan Da’ish taimakon makamai a yankin Al’anbar da Falluja.

Jami’in ya kara da cewa; wannan ba shine karo na farko ba da kasashen hadin gwiwa karka shin jagoranci Amurka ke kokarin aikama yan ta’addan Da’ish da tai makon makaman yaki ta hanyar jirage masu saukar angulu ba, wanda hakan ke tabbatar da cewa Amurka ce ta kafa yan ta’addan Da’ish da nufin wargaza kasar ta Iraki.ABNA